May 20, 2024

Binciken jin ra’ayin Jama’a da na kasuwanni ya nuna cewa farashin Masara da Dawa da sauran hatsi ya fara sauka a jihar katsina da makwabtanta

Ministan Noma Abubakar Kyari Ya Gana Da Manyan Masu Ruwa Da Tsaki A Fannin Noma Domin Shirye-Shiryen Noman Rani Da Na Damina Mai Zuwa.

Ganawar ta tabo yadda za a yi rabon taki da sauran kayan noma ga manoma don tabbatar da an sami wadataccen abinci a kasa.

An yi Amfani da sanya hannun tsohon Shugaba Buhari na Bogi wajen sace kwatancin Naira Bilyan 80 da shida daga babban bankin kasa.

Tsohon Sakataren Gwamnati Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a yayinda yake bayar da shaida kan damfarar Dala Milyan 6.2 da ake zargin Emefele da yi a yayinda yake gwamnan babban bankin

A Wani binciken na daban an gano cewa Dala Bilyan hudu da rabi da doriya sun yi batan dabo daga babban bankin kasa a shekarar 2019 inda aka gano kudin da ke asusun a shekarar 2018 ya ragu daga Dala Bilyan 42.59 zuwa Dala Bilyan 38.09. Kana an rasa gane inda Bankin na CBN ya adana kudaden da aka karbo daga manyan barin kasa na wancan lokacin.

Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da shirin Farfado da wasu jihohin Arewa da rikici ya ďaiďaita karkashin sabon shirinta mai Suna Pulako Initiative.

Shi dai wannan shiri za a gudanar da shi ne a jihohi bakwai da suka hada da Sokoto, Kebbi, Zamfara, Kaduna Katsina, Neja, da Benue.

Shirin zai kunshi sake samar da yankuna na musamman ga manoma da makiyaya tare da samar musu da ababen more rayuwa da suka hada da gidaje. Makarantu, lantarki, Asibitoci, Hanya, da tsaro

Ministan Yada Labarai Malam Idris Malagi Ya mayar da martani da kakkausar Murya ga taron Gwamnonin PDP wanda ya gudana a jahar Bauchi. Ministan ya roki gwamnonin da maimakon zargin gwamatin tarayya da janyo tsadar rayuwa gara su mai da hankali wajen yin amfani da karin kudaden da Gwamnatin shugaba Tinubu ta yi musu wajen inganta rayuwar al’ummar jihohinsu da rage musu matsin tattalin arziƙi ta hanyar biyan basussukan albashi da fansho da garatuti da ma bayar da mafi karancin albashi na dubu 30 da ministan yace gwamnonin Na PDP sun yi kaurin suna wajen gaza yin hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *