January 27, 2023

Daga Ibrahim Garba Nayaya

A safiyar ranar Alhamis din da ta gabata ne wani bawan Allah mai suna Muhammad Tukur Muhammad Nguru ya tsinci jaririya haihuwar uwarta, tsirara babu koda tsumma ne da zai kare mata sanyin Asubashi, ko rabar da ke nashe a sakamakon ruwan sama.

Wannan al’amari kuwa, ya afku ne a unguwar Bubari, ta cikin Sabon Gari Kanuri dake Karamar Hukumar Nguru ta Jihar Yobe, karamin wani layin da ba kowa ne me bin sa ba, kudu da makarantar firamare ta Bubarin.

Masu karatu me zaku ce game da irin wannan rashin imanin da ake yi?

Leave a Reply

Share via
Copy link
Powered by Social Snap